Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa daliban manyan makarantun sakandare da ke bin bangaren fasaha da al’adun gargajiya (arts & humanities) ba lallai ne su sami sakamako na “credit” a Mathematics ba kafin su samu gurbin shiga jami’a ko kwalejojin kimiyya a Najeriya. Wannan mataki, kamar yadda Ma’aikatar Ilimi ta bayyana a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta, Folasade Boriowo, ta fitar, na cikin sabbin ka’idojin shigar dalibai makarantu na gaba da sakandare da aka sabunta.
A cewar sabbin ka’idojin, daliban jami’a za su bukaci akalla “credit” biyar cikin darussa masu dacewa da fannin da za su karanta, ciki har da Turanci, amma Mathematics za ta kasance wajibi ne kawai ga bangarorin kimiyya, fasaha da zamantakewa. A matakin polytechnic kuma, daliban fannin kimiyya ne kawai za a bukaci su samu Mathematics yayin da sauran fannonin za su bukaci Turanci kawai. Haka zalika, a matakin HND da NCE akwai bambance-bambance bisa nau’in shirin karatu.
Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya bayyana cewa wannan sauyi na nufin rage shingayen da ke hana dalibai shiga jami’a da fadada damar samun ilimi a matakin gaba da sakandare. Ya ce gwamnati ta amince da cikakken sauye-sauyen tsarin shigar dalibai domin kara yawan wadanda ake karɓa daga kusan 700,000 a kowace shekara zuwa sama da miliyan daya.
Gwamnati ta ce sabon tsarin zai ba da damar karin dalibai kimanin 250,000 zuwa 300,000 a kowace shekara su sami gurbin karatu a jami’o’i, polytechnics, da kwalejojin ilimi a fadin kasar. Wannan sauyi ya biyo bayan dogon lokaci na takura da ya hana dubban dalibai masu cancanta damar ci gaba da karatu saboda shingayen samun Mathematics.
