Gwamnatin Tarayya ta kammala horaswa tare da tura dakaru sama da 7,000 na gandun daji domin ƙarfafa tsaro da kare dazuzzuka daga ’yan ta’adda. An horas da su ne ƙarƙashin shirin Presidential Forest Guards Initiative da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar a watan Mayun 2025.

An ce sabbin jami’an sun fito ne daga jihohi bakwai da ke kan gaba wajen fuskantar matsalolin tsaro, ciki har da Borno, Sokoto, Yobe, Adamawa, Niger, Kwara da Kebbi. Shugaban Tsaro na Ƙasa, Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa za su zama masu tattara bayanan sirri da kare al’umma tare da taimaka wa hukumomin tsaro kwato yankunan da ’yan bindiga suka mamaye.

Shirin horon ya haɗa da dabarun tsaro, sintiri mai nisa, ceto da farmakin kwanton bauna, inda aka ce tura su aiki zai fara nan take. Gwamnati ta jaddada cewa za a faɗaɗa shirin zuwa ƙasa baki ɗaya domin magance garkuwa da mutane, fashi da kuma amfani da dazuzzuka wajen aikata laifuka.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version