Gwamnatin Tarayyar Najeriya tayi Allah-wadai da harin da ’yan bindiga suka kai wa Makarantar Sakandiren ’Yan Mata ta Maga, a Jihar Kebbi, harin da ya yi sanadin kashe jami’an makarantar da kuma sace ɗalibai 25. Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa wannan al’amari abin bakin ciki ne, tare da bayyana irin kokarin da gwamnati ke yi wajen ganin an kubutar da yaran cikin koshin lafiya.

A cewar ministan, gwamnatin tarayya ta umarci jami’an tsaro da hukumar tattara bayanan sirri da su tashi tsaye wurin bin diddigin inda aka boye ɗaliban domin tabbatar da kuɓutar da su ba tare da wani cikas ba. Ya ce an ɗauki duk matakan da suka dace don ganin an bi hanyoyi mafi aminci wajen aiwatar da aikin ceto.

Gwamnatin ta kuma nuna alhinin ta ga iyalan waɗanda abin ya shafa, musamman ma iyayen ɗaliban da aka sace. Mohammed Idris ya ce gwamnati na tare da su a wannan mawuyacin hali, kuma tana jin zafin abin da ya faru matuƙa.

A ƙarshe, ministan ya tabbatar wa al’umma cewa gwamnati ba za ta yi wasa da tsaron rayuka da dukiyoyin ’yan ƙasa ba, tare da ba da tabbacin cewa za a cigaba da yin aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro domin kawo ƙarshen irin waɗannan hare-hare a faɗin ƙasar.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version