Sabon shugaban rikon-kwarya na bangaren PDP na Turaki, Kabiru Turaki, ya roki Shugaban Amurka, Donald Trump, da sauran ƙasashen duniya su shiga tsakani domin tsame Najeriya daga rikicin siyasa da yake kara kamari. Turaki ya ce demokaradiyyar kasar na fuskantar babbar barazana yayin da rikicin cikin gidan jam’iyyar ya rikide zuwa tashin hankali a Abuja.

A jawabin da ya yi a gaban ‘yan jarida a Wadata Plaza, Turaki ya zargi bangaren Ministan Abuja, Nyesom Wike, da turo ‘yan daba masu dauke da makamai domin hana su shiga hedkwatar jam’iyyar. Ya ce halin da ake ciki ya kai matsayin da ake bukatar kulawa ta duniya saboda yana barazana ga zaman lafiya da tsarin siyasa.

Turaki ya kara jaddada cewa bangarensu ya shirya sadaukar da rayuwarsu domin kare kujerunsu da kuma demokaradiyyar ƙasar. Wannan furuci nasa ya zo ne mintuna kafin rikici ya barke tsakanin bangarorin biyu da suka shirya zaman NEC da BoT a rana ɗaya, lamarin da ya janyo harbe-harben barkonon tsohuwa da firgita jama’a.

Bayan fitar da hayaki me sa hawaye, magoya baya da ma’aikata da ‘yan jarida sun watse da gudu, yayin da sabanin ra’ayi tsakanin bangarorin Turaki da Anyanwu ya kara ta’azzara. Wannan rikici ya tabbatar da tabarbarewar da PDP ke ciki, yayinda ake ci gaba da fargabar yadda rikicin zai shafi siyasar Najeriya baki ɗaya.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version