Gwamnatin Tarayya ta amince da kashe akalla Naira tiriliyan 1.92 domin inganta filayen jiragen sama a fadin Najeriya cikin shekaru biyu, tun bayan fara zaman Majalisar Zartarwa ta Kasa (FEC) a ranar 28 ga Agusta, 2023, karkashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Rahoton Sunday PUNCH ya nuna cewa kudaden sun shafi sayen na’urorin tsaro, tsarin kula da zirga-zirgar jiragen sama, inshorar kadarori, da kuma manyan ayyukan gyara da sake gina filayen jiragen sama.
Daga cikin manyan ayyukan da aka amince da su akwai sake gina gaba daya tsohon ginin Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed a Legas (Terminal 1), gyaran runways da taxiways a Legas, Kano da Fatakwal, da kuma girke na’urorin zamani na haske da tsaro (CAT II lighting). Haka kuma, an amince da sayen na’urorin gano miyagun kwayoyi da abubuwan fashewa a manyan filayen jiragen sama, domin rage wahalar binciken fasinjoji da kuma inganta tsaro, a cewar Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo.
Rahoton ya kara da cewa an amince da kudade masu yawa don cibiyoyin umarni da kulawa, sabunta na’urorin sadarwa da hangen motsin jirage, da kuma kara amfani da fasahar tantance bayanan fasinjoji (biometric e-gates). Gwamnatin ta bayyana cewa wadannan kudade na daga cikin kokarin da ake yi na daidaita filayen jiragen saman Najeriya da ka’idojin Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Duniya (ICAO), tare da inganta tsaro, rage jinkiri da kara amincewar fasinjoji da harkar sufurin jiragen sama a kasar nan.
