Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya soki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan yadda take tafiyar da tattalin arzikin Najeriya, yana mai cewa babu wata kididdiga da za ta iya ɓoye halin ƙuncin da ’yan ƙasar ke ciki.

Atiku ya ce gwamnatin na ƙoƙarin nuna cewa cire tallafin man fetur da sauran sauye-sauyen tattalin arziki sun kawo sauƙi, amma ya yi zargin cewa bashin gwamnatin tarayya ga Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ƙaru maimakon ya ragu.

Ya kuma ce gwamnatin ba ta cika wasu daga cikin alƙawuran da ta ɗauka kan sabon mafi ƙarancin albashi da wasu alawus-alawus na ma’aikata ba.

Atiku ya ce ƙungiyoyin ƙwadago ne ke ci gaba da yin korafi kan waɗannan batutuwa, yana mai sukar yadda gwamnatin ke bayyana halin tattalin arzikin ƙasar.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version