Gwamnonin Arewa sun bayyana alhinin su kan rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci kuma jagoran darikar Tijjaniyya na duniya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi. Shugaban kungiyar, Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ce marigayin malami ne mai zurfin ilimi da ya shafe tsawon shekara ɗari yana yada ilimi da tarbiyya ga al’umma.

A cikin sanarwarsa, Gwamna Yahaya ya bayyana cewa Sheikh Dahiru Bauchi ya yi manyan tasiri a fannonin Qur’ani, Hadisi, fikihu da tasawwufi, inda koyarwarsa ta shafi rayuwar miliyoyin mutane. Ya ce malamin ya kasance mutum mai sauƙin kai da tsantseni kuma abin koyi ga masu bin darikar Tijjaniyya da sauran musulmi.

wannan rahoton ya nuna yadda marigayi Sheikh Dahiru ya taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa zaman lafiya, haɗin kai, da ɗabi’u nagari a Arewa da ma ƙasar baki ɗaya. Bechi Hausa ta tattaro cewa gwamnoni sun bayyana cewa rayuwarsa cike take da hidima ga addini da ɗan Adam.

Gwamnonin Arewa sun miƙa ta’aziyyarsu ga iyalan marigayin, al’ummar Tijjaniyya da daukacin musulmi, tare da roƙon Allah Ya jikansa Ya ba shi Aljannatul Firdaus.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version