Gwamnonin jihohin Arewa 19 suna gudanar da taron gaggawa a Kaduna kan yawaitar sace-sace da karuwar ta’addanci. Taron na gudana ne a gidan gwamnati na Sir Kashim Ibrahim, inda ake tattauna yadda hare-haren ’yan bindiga da garkuwa da mutane ke ƙaruwa.
Manyan gwamnonin da suka halarci taron sun haɗa da Uba Sani na Kaduna, Bago na Neja, Inuwa Yahaya na Gombe da Umar Namadi na Jigawa. Yayin da sauran gwamnonin suka tura mataimakansu a matsayin wakilai.

Shugabannin gargajiya, ciki har da Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III, sun kasance a wurin domin bayar da shawarwari. Majiyoyi daga gwamnatin jihar sun ce ana mayar da hankali ne kan matsalar sace dalibai da ƙona makarantu da ke sake dawowa cikin yankin Arewa.
A kwanakin baya, an yi garkuwa da ɗalibai 24 a Makarantar GGC Maga ta Kebbi, tare da kashe mataimakin firamare. Bayan kwana kaɗan kuma, ’yan bindiga sun kai hari a Papiri, Jihar Neja, inda suka sace sama da mutum 300.

Taron ya kuma yi la’akari da rufe makarantu da dama da gwamnatoci suka yi saboda tsananin barazanar tsaro. Bechi Hausa ta tattaro cewa gwamnonin na neman tsayar da tsari guda na hadin gwiwar jihohi domin dakile matsalar.
A cewar majiyoyi, an buɗe tattaunawa kan ƙarfafa tsaro a makarantun sakandare da na firamare saboda barazanar hare-haren da ke ƙaruwa. Wannan mataki na zuwa ne bayan sace-sacen da suka girgiza Arewa a makonnin baya.

A yanzu dai ana sa ran fitar da sanarwar karshe daga taron domin bayyana matakan da za a ɗauka. Masu sharhi na ganin cewa idan aka aiwatar da shawarwarin da aka tattauna, zai iya rage yawaitar ayyukan ta’addanci a sassan Arewa.
Mutane da dama na kallon taron a matsayin wani muhimmin mataki da zai ƙara karfafa haɗin kai tsakanin gwamnatoci da shugabannin gargajiya. Gwamnonin Arewa dai sun ce za su ɗauki dukkan matakai don kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version