Wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) daga yankin arewacin Najeriya sun amince da tsohon minista, Kabiru Tanimu Turaki, a matsayin ɗantakararsu a babban taron jam’iyyar da za a gudanar cikin watan Nuwamba. Wannan mataki, a cewar jam’iyyar, ya biyo bayan doguwar tattaunawa da tuntuɓar juna tsakanin manyan mambobi da masu ruwa da tsaki daga yankin.
Mataimakin sakataren yaɗa labaran PDP na ƙasa, Ibrahim Abdullahi, ya tabbatar da hakan a wata hira da BBC, inda ya bayyana cewa gwamnonin PDP daga arewacin ƙasar ne suka jagoranci yanke shawarar. Ya ce an cimma matsaya ɗaya ne domin ƙarfafa haɗin kai da gujewa rabuwar kai a lokacin babban taron jam’iyyar.
Wannan na nuna cewa yankin arewa ya samu matsaya ɗaya kan wanda zai wakilce su a zaɓen shugabancin jam’iyyar, wanda aka shirya gudanarwa a ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamba. Ana sa ran wannan mataki zai taka muhimmiyar rawa wajen ƙayyade shugabancin jam’iyyar a sabon zagayen.
