Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ta yi watsi da bukatar da tsohon mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Abba Kyari, da ‘yan uwansa biyu suka gabatar don a wanke su daga shari’ar da Hukumar NDLEA ta shigar a kansu kan boye dukiya da kuma karkatar da kudaden haram.
Mai shari’a James Omotosho ya bayyana cewa hujjojin da hukumar NDLEA ta gabatar — ciki har da shaidu 10 da takardu fiye da 20 — sun isa su kafa prima facie, wato hujja ta farko da ke nuna akwai dalilin da ya sa wadanda ake tuhuma za su bayar da kariya. Ya ce wannan ba yana nufin an same su da laifi ba ne, amma yana nuna cewa akwai bukatar su bayyana nasu bangaren don tabbatar da gaskiya.
Kyari da ‘yan uwansa sun ce babu hujja da ta nuna suna da hannun jari a kadarorin da ake tuhuma da su, tare da jaddada cewa babu takardun shaidar mallaka da kotu za ta dogara da su. Sai dai mai shari’a ya ce a wannan mataki kotu ba za ta tantance karfin hujjoji ba, illa dai ta tabbatar da cewa akwai abin da ya wajabta a saurari kariya daga wadanda ake zargi.
Alkalin ya umurci Abba Kyari da ‘yan uwansa su kare kansu cikin kwanaki uku, tare da dage sauraron karar zuwa Nuwamba 4, 5 da 6 domin ci gaba da shari’a. Ya kara jaddada cewa suna da cikakken ‘yancin kare kansu bisa tsarin kundin tsarin mulki na 1999, kuma suna ci gaba da kasancewa maras laifi har sai an tabbatar da akasin haka.
