Tsohon Antoni-Janaran Najeriya, Abubakar Malami (SAN), ya bayyana cewa EFCC ta ci gaba da tsare shi ne saboda soke belin da ta yi masa ba tare da ta nuna cewa ya karya wani sharadi ba. Malami ya kai kansa ofishin hukumar ne ranar Litinin domin amsa tambayoyi, amma aka sanar da shi cewa an soke belinsa tare da gindaya masa sabbin sharudda da yake cewa yana da niyyar cikawa.

Malami, ta bakin mai taimaka masa na musamman, Mohammed Bello Doka, ya karyata zarge-zargen da ake yadawa, ciki har da na daukar nauyin ta’addanci da mallakar asusun banki 46, yana mai cewa labaran karya ne da ake amfani da su domin bata masa suna. Ya ce ko a sau daya ba a taba tambayar sa kan zargin daukar nauyin ta’addanci ba, kuma tsohon hafsan sojan da aka alakanta da zargin ya musanta hakan.

Ya kuma yi karin haske kan batun kudaden Abacha, inda ya ce gwamnatin Buhari ta ki amincewa da sharuddan lauya Enrico Monfrini, shi kuma ya sake tattaunawa da lauyoyin cikin gida wadanda suka yarda da kaso 5 kacal—abin da ya ce ya ceci Najeriya dimbin kudade. Haka kuma ya ce dukkan kudaden da aka dawo da su an yi amfani da su ne bisa ka’ida tare da kulawar kasashen duniya.

EFCC na cigaba da tsare Malami kan wasu bincike da ke gudana, ciki har da batun dawo da kudaden Abacha da kuma yadda aka yi amfani da kudaden tallafin al’umma. Malami dai ya ce zai ci gaba da bin doka tare da cika duk wani sabon sharadi da hukumar za ta bukata.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version