Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin ƙara tsaurara matakan tsaro a jihar Borno, biyo bayan harin bam da aka kai a Masallacin Al-Adum da ke kasuwar Gamboru a Maiduguri. Harin, wanda ake zargin ‘yan ta’adda ne suka kai shi da misalin ƙarfe 6 na yamma a ranar Laraba, ya yi sanadin mutuwar mutane biyar tare da jikkata wasu da dama yayin da masu ibada ke sallar magariba.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis, Shettima ya yi kakkausar suka ga harin, inda ya bayyana shi a matsayin mummunan ta’adi da aka aikata kan fararen hula da zaman lafiyar ƙasa. Ya ce gwamnatin tarayya na tura ƙarin rundunonin tsaro na musamman zuwa Maiduguri domin farautar waɗanda suka aikata laifin tare da tabbatar da kare al’umma da muhimman kadarorin jama’a a Arewa maso Gabas.

Mataimakin shugaban ƙasar ya jaddada cewa gwamnatin Tinubu ba za ta lamunci duk wani yunkuri na kawo cikas ga tsaron ƙasa ba, yana mai tabbatar da cewa jami’an tsaro na aiki dare da rana domin ganin an cafke masu hannu a harin tare da hukunta su bisa doka. Ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga gwamnatin Borno, mazauna yankin da iyalan waɗanda suka rasa rayukansu, yana mai tabbatar da cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da ba da dukkan goyon bayan da ake buƙata domin murkushe ta’addanci a kowanne irin salo.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version