Hukumar Ƙididdiga ta Kasa (NBS) ta bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya ci gaba da raguwa, inda ya sauka zuwa kashi 16.05% a watan Oktoba 2025. Wannan sauki ya nuna cigaba a kokarin da ake yi na daidaita farashi da rage matsin tattalin arziki ga al’umma.
A cewar rahoton wata-wata da hukumar ta fitar, sabuwar alkalumar ta nuna raguwar hauhawar farashin da kashi 1.97% idan aka kwatanta da kashi 18.02% na watan Satumba. Wannan na nuni da cewa matsin farashi na cikin sauki idan aka kwatanta da watannin baya.
NBS ta ce raguwar na da alaƙa da wasu matakai da gwamnati ke dauka na farfado da tattalin arziki da kuma karuwar samar da kayayyaki a kasuwa. Haka kuma masana sun bayyana wannan ci gaba a matsayin alamar dawo dawowar daidaito a fannin kasuwanci da farashi a Najeriya.


