Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan Najeriya, Honarabul Alhassan Ado Doguwa, ya bayyana cewa bidiyon da ya yadu a kafafen sada zumunta yana yin kaikomo da ƙwambo ba don wasa ba ne, sai don aikewa da saƙo ga abokan hamayyarsa na siyasa.

A wata tattaunawa da ya yi da BBC a birnin Landan, Doguwa ya ce ya shirya bidiyon ne don nuna wa maƙiyansa, musamman na yankinsa Doguwa da Tudun Wada, cewa duk da adawa da suke yi masa, har yanzu shi ne wakilinsu kuma yana nan daram.

Ya bayyana cewa, tafiyarsa Landan da kuma bidiyon da ya ɗauka suna nufin nuna farin ciki da samun nasara duk da ƙoƙarin wasu ‘yan adawa na kawo masa cikas a harkar siyasa. A cewarsa, bidiyon wani irin “cali-cali” ne da ke nuni da ƙarfin gwiwa da cigaba.

Doguwa ya kuma ƙara da cewa, wannan bidiyo wata hanya ce ta nuna cewa siyasa ba wai gaba da ƙiyayya ba ce, illa kawai fafutukar neman ci gaba da wakiltar jama’a bisa gaskiya da amana.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version