Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ayyana Farfesa Chukwuma Charles Soludo na jam’iyyar APGA a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Anambra da aka gudanar a ranar 8 ga Nuwamba 2025. Sakamakon da aka bayyana a cibiyar tattara sakamako da ke Awka ya nuna cewa Soludo ya samu kuri’u 422,664, wanda ya fi na sauran ‘yan takarar zaben da tazara mai yawa.

Dan takarar APC, Nicholas Ukachukwu, ya zo na biyu da kuri’u 99,445, sai George Moghalu na LP da kuri’u 10,576, yayin da Jude Ezenwafor na PDP ya tashi da kuri’u 1,401. Returning Officer na zaben, Farfesa Edoba Omoregie, ya ce zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali kuma Soludo ya cika duk sharuddan da doka ta tanada.

Magoya bayan jam’iyyar APGA sun yi murna da sakamakon, suna cewa nasarar alama ce ta cigaba da goyon bayan jama’a ga gwamnatinsu. Sai dai akwai yiwuwar wasu jam’iyyu su yi nazari kan sakamakon domin yanke shawarar kai koke ko akasin haka.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version