Hukumomin Iran sun sanar da naɗin Alireza Arafi a matsayin jagoran addinin ƙasar na riƙo, har sai an zaɓi sabon jagora. Matakin ya biyo bayan rasuwar jagoran addini Khamenei, inda ake shirin bin tsarin doka domin cike gurbin.

Majalisar manyan malaman ƙasar mai mambobi 88 ce ke da alhakin zaɓen sabon jagoran addini. Al’ummar ƙasar ne ke zaɓar mambobin wannan majalisa duk bayan shekara takwas, kamar yadda dokokin ƙasar suka tanada.

Sai dai ana ganin zaɓen sabon jagoran ba zai kasance mai sauƙi ba, sakamakon rashin kwanciyar hankali da ƙasar ke fuskanta a halin yanzu. Masu lura da al’amura na cewa yanayin yaƙin da ake ciki na iya shafar yadda za a gudanar da zaɓen cikin natsuwa.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version