Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa Isra’ila ta amince da janye dakarunta daga wasu sassa na Zirin Gaza a matakin farko na yarjejeniyar zaman lafiya tsakaninta da kungiyar Hamas.
A cewar Trump, cikin kwanaki uku na farko bayan fara aiwatar da yarjejeniyar, Hamas za ta sako dukkan ragowar Isra’ilawa da take rike da su — ko a mace ko a raye — yayin da Isra’ila kuma za ta saki kimanin fursunonin Falasdinawa 2,000, ciki har da kusan 300 da aka yanke wa hukuncin kisa.
Sai dai wakiliyar BBC ta ruwaito cewa Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana cewa yana sa ran sakin fursunonin zai gudana ne yayin da dakarun Isra’ila za su ci gaba da kasancewa a cikin Gaza — matsayi da kungiyar Hamas ta yi watsi da shi.
A halin yanzu, surukin Trump, Jared Kushner, tare da wakilinsa na musamman Steve Witkoff, sun nufi Masar domin ganawa da wakilan Hamas. Wannan ganawar dai na da nufin kammala tattaunawa kan wasu batutuwan da kungiyar ta bukaci a sake nazari a kansu, kafin rattaba hannu kan yarjejeniyar ta karshe.
