Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa Jihar Borno ce ta fi sauran jihohin Najeriya yawan mutanen da suka kammala rajistar katin zabe ta yanar gizo a mako na tara na rajistar da ake gudanarwa a fadin ƙasar. Bayanai daga hukumar sun nuna cewa cikin jimillar mutane 8,003,196 da suka kammala rajistar kan layi, Borno ta samu mutum 826,130, wanda shi ne adadi mafi girma a fadin ƙasar.

Jihohin Osun da Lagos sun biyo baya da mutane 646,580 da 604,819 bi da bi, yayin da Kebbi ta samu 581,135, Kaduna kuma 510,490. Ogun ta biyo da 510,062, sannan Kano ta samu 421,941. Haka kuma Kogi ta samu 361,233, Zamfara da Yobe kuma suka samu 304,065 da 292,714 bi da bi.

A cewar INEC, jimillar mutane 1,710,450 ne suka kammala cikakken rajista a kasar – waɗanda suka haɗa da masu rajista ta yanar gizo (956,566) da kuma waɗanda suka yi rajista kai tsaye (753,884). Hukumar ta kuma tabbatar da cewa rajistar masu jefa ƙuri’a a Jihar Anambra ta dakata har sai bayan zaɓen gwamna da za a gudanar a ranar 8 ga Nuwamba, 2025, kamar yadda sashen 9(6) na dokar zaɓe ta 2022 ya tanada.

Rahoton ya kuma nuna cewa a baya jihohin kudu maso yamma irin su Osun, Lagos, da Ogun ne ke kan gaba tun bayan fara rajistar a ranar 18 ga Agusta, 2025. Sai dai a yanzu an samu tashin gwuiwa daga jihohin arewaci musamman Borno da Kebbi, sakamakon ƙoƙarin ƙungiyoyin al’umma, shugabannin addini da kuma hukumomi wajen wayar da kan jama’a domin karfafa su yin rajista.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version