Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Ƙasa (NERC) ta bayyana cewa kamfanonin rarraba wutar lantarki 11 sun yi asarar kusan Naira biliyan 358 a zango na biyu na shekarar 2025, sakamakon gibin biyan kuɗi da rashin biyan kuɗin wuta daga abokan ciniki.

A rahoton ta, NERC ta ce an tara Naira biliyan 546.71 daga cikin jimillar Naira biliyan 909.59 da aka rarraba, wanda bai kai kashi 60% na wutar da aka tura musu ba. Wannan ya haifar da gibin kuɗi na Naira biliyan 167.25, tare da rashin biyan kuɗin wuta da ya kai Naira biliyan 190.64 daga abokan ciniki.

Kamfanin Eko ne ya fi kowa inganci da kashi 96.67%, yayin da Yola ta fi ƙasa da kashi 58.38%. Haka kuma, yawancin kamfanonin sun fi karkata wajen bai wa ‘yan kasuwa wuta fiye da gidaje, sai na Fatakwal kaɗai da ya bi tsarin hukumar.

Gwamnatin tarayya ta kuma ɗauki nauyin tallafi na Naira biliyan 514.35, wanda ya ragu da kaso 4.11% idan aka kwatanta da zangon farko na 2025.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version