Wani sabon bincike ya gano cewa yawancin mata da ke fuskantar hukuncin kisa a Najeriya iyaye ne, kuma masu fama da talauci, rashin ilimi. Binciken wanda aka gabatar a taron tabbatar da sakamako a Abuja ranar Litinin, an gudanar da shi ne ta Hope Behind Bars Africa tare da hadin gwiwar Hukumar Kare Hakkokin Dan Adam ta Kasa (NHRC) da tallafin World Coalition Against the Death Penalty da French Development Agency.

Rahoton ya nuna cewa kashi 47% na matan da aka yankewa hukuncin kisa su na tsakanin shekaru 18 zuwa 35, yayin da fiye da kashi ɗaya bisa uku ba su da ilimi kwata-kwata, sai kuma kashi 10% kacal suka kai matakin gaba. Haka kuma, kashi 70% daga cikinsu iyaye ne da suka bar ‘ya’yansu cikin mawuyacin hali da rashin kulawa, abin da ke kara tsananta matsalolin zamantakewa ga iyalansu. Yawancinsu sun taba fuskantar cin zarafi kamar auren dole da dukan aure.

Binciken ya kuma nuna cewa kashi 75% daga cikin matan ba su san dokar da aka gurfanar da su a karkashinta ba, yayin da kashi 85% suka ce tsarin dokokin ya nuna wariya ga mata. Fiye da rabin matan sun bayyana cewa shari’unsu ba su kasance a bude ba, kuma tsarin shari’a mai rinjayen maza ya shafi sakamakon shari’unsu. Haka kuma, yawanci sun fuskanci tsangwama da kin amincewa daga mazajensu da al’ummarsu bayan gurfanar da su, musamman a shari’o’in da suka shafi zina ko laifukan jima’i.

Shugaban NHRC, Dr. Tony Ojukwu (SAN), ya yi kira da a aiwatar da sauye-sauye cikin gaggawa tare da jaddada matsayinsu na adawa da hukuncin kisa. Ya bayyana hukuncin kisa a matsayin mataki da bai dace da tsarin kare hakkin dan Adam ba kuma bai rage laifuka yadda ake zato ba. Rahoton ya ba da shawarwari da suka hada da kafa moratorium kan aiwatar da hukuncin kisa, yin gyare-gyaren dokoki masu la’akari da jinsi, bunkasa tallafin shari’a da inganta yanayin zaman kurkuku. Wannan bincike ya zo ne a lokacin bikin Ranar Duniya ta Adawa da Hukuncin Kisa, wanda ake gudanarwa a duk shekara ranar 10 ga Oktoba.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version