Kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano (KEDCO) ya nuna damuwa kan matsalolin samar da wuta daga kamfanin wutar lantarki na ƙasa da TCN zuwa jihohin Arewa maso Yamma. Ya bukaci gwamnatin tarayya ta umarci TCN da ya ba fifiko ga manyan ayyukan layin wuta da gyare-gyare domin inganta isar da wuta.

Kamfanin ya ce a halin yanzu hanyoyi biyu ne kacal ke kai wuta zuwa cibiyar Kano ta Kaduna da Jos, lamarin da ke sa tsarin cikin haɗarin katsewa. Ya ƙara da cewa ana buƙatar ƙara tsaro da faɗaɗa layin Shiroro zuwa Mando har zuwa Kano domin rage yawan ɗaukewar wuta.

KEDCO ya ce katsewar wuta a ƙarshen mako na ƙaruwa sakamakon ayyukan gyara da girka na’urorin OPGW, abin da ke shafar masana’antu da rayuwar jama’a. Ya kuma bayyana cewa yana aiki da hukumomin lantarki domin daidaita hidima, tare da hanzarta shirye-shiryen ƙara samar da wuta a cikin gida.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version