Fadar shugaban ƙasa ta bayyana sauya sheƙar gwamnan Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), a matsayin babbar koma baya ga burin Atiku Abubakar na takarar shugaban ƙasa.

Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya ce sauya shekar Fintiri na nuna cewa Atiku ba shi da cikakken farin jini a jiharsa ta asali. Sanarwar ta ce gwamna Fintiri ya ɗauke duk wata ƙarfi da Atiku ke da ita a jiharsa, kuma ɗan takarar da ba shi da ƙarfi a garinsa ba zai iya tallata kansa a sauran yankuna ba.

Fadar ta kuma shawarci Atiku da ya yi tunanin yin ritaya daga siyasa, tare da komawa “gidansa na biyu” a birnin Dubai. Sanarwar ta nuna cewa yayin da zaɓen shugaban ƙasa ke ƙaratowa cikin ƙasa da shekara guda, sauya sheƙar Fintiri na daga cikin manyan matsalolin da ka iya shafar shirin Atiku na sake tsayawa takara, tana mai cewa wannan lamari babbar barazana ce ga burinsa na siyasa.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version