Mai ba tsohon gwamnan Kaduna shawara kan yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ya ce kotu ta ɗage shari’ar da ake yi da shi zuwa 23 ga Afrilu, 2026. An ɗage shari’ar ne bayan kasa gabatar da shi a gaban Babbar Kotun Tarayya Abuja kamar yadda aka tsara.

Mai gabatar da ƙara ya roƙi kotu ta ba da makonni biyu domin DSS ta gabatar da El-Rufai, wanda ke hannun ICPC. Sai dai lauyansa, Wole Iyamu, ya ce babu dalilin ƙarin lokaci tun da yana tsare a hannun gwamnati.

Alƙali, Joyce Abdulmalik, ta amince da ɗage shari’ar zuwa Afrilu, duk da cewa ya zarce abin da aka nema. Rahotanni sun ce yana tsare tun 16 ga Fabrairu bayan amsa gayyatar EFCC, kafin daga bisani ICPC ta karɓe shi, kuma har yanzu ba a ba da belinsa ba.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version