Kotun Tarayya da ke Abuja ƙarƙashin Alƙali Emeka Nwite ta amince da bayar da belin tsohon Babban Lauyan Ƙasa kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, tare da matarsa da ɗansa kan kuɗi ₦500m kowannensu.
Kotun ta shimfiɗa ƙa’idoji masu tsauri, inda ta umarci kowanne daga cikinsu ya kawo mutane biyu da za su tsaya musu, masu filaye a Maitama, Asokoro ko Gwarimpa, tare da miƙa takardun filayen domin tantancewa, da kuma ajiye fasfofinsu a kotu.
Malami na fuskantar tuhume-tuhume 16 na halasta kuɗaɗen haram da EFCC ta shigar, lamarin da ya shafi ma’amaloli da ake zargin darajarsu ta kai kusan naira biliyan 9, yayin da kotu ta ɗage sauraron shari’ar zuwa 17 ga Fabrairu, tare da umartar a ci gaba da tsare shi a gidan gyaran hali na Kuje har sai an cika sharuɗɗan beli.
