Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da belin Naira biliyan biyu ga Shugaban Ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta Ƙasa, Bello Bodejo. Kotun ta kuma umarci ya gabatar da masu tsaya masa biyu da kowannensu zai ɗauki nauyin kuɗin belin iri ɗaya.

Mai shari’a Inyang Ekwo ya ce ɗaya daga cikin masu tsayawa belin dole ne ya mallaki kadara a yankin Abuja Municipal Area Council (AMAC), sannan ɗaya daga cikinsu ya gabatar da shaidar biyan haraji na shekarun 2023, 2024 da 2025. Haka kuma kotun ta umarci magatakarda ya tantance dukkan takardun kafin a cika sharuddan belin.

Kotun ta kuma umarci Bello Bodejo ya miƙa fasfo ɗinsa tare da hana shi fita daga Najeriya ko wajen ikon kotun ba tare da izini ba. Daga nan sai aka ɗage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranakun 5, 6 da 7 ga Oktoban 2026, yayin da yake fuskantar tuhume-tuhume 12 da suka shafi zargin wanke kuɗaɗe da suka kai dala miliyan 2.33.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version