Mai Bai Wa Shugaba Bola Tinubu Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Sadarwa, Daniel Bwala, ya ce dakarun sojin Najeriya sun kama wasu baƙin ƙasashen waje da ake zargin suna da alaƙa da matsalolin tsaro a wasu sassan ƙasar. Ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa a shirin The Link Up Podcast.
Bwala ya ce gwamnati da sojoji sun ɓoye bayanan waɗanda aka kama da ƙasashensu saboda dalilan tsaro da kuma hulɗar diflomasiyya.
Ya kuma ce gwamnatin tarayya na ƙoƙarin dakile yaɗuwar ayyukan Boko Haram da ISWAP zuwa wasu yankunan ƙasar. Bwala ya musanta zargin cewa sojoji na kare ‘yan ta’adda, yana mai cewa gwamnati ta gyara matsalolin haɗin gwiwa da ake samu tsakanin rundunar soji da ta sama, tare da yabawa gwamnatin Shugaba Tinubu kan matakan da take ɗauka wajen inganta tsaro.
