Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da wasu shugabannin PDP suka shigar domin tilasta wa INEC ta amince da kwamitin riƙon ƙwarya na jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin Kabiru Turaki.
Alƙali Salim Ibrahim ya ce masu shigar da ƙarar ba su da hurumin gabatar da ita, saboda haka kotun ba ta da ikon sauraron shari’ar. Ya kuma bayyana cewa sun kasa tabbatar da cewa INEC ta taɓa amincewa da kwamitin da suke goyon baya.
Shugaban Kwamitin Amintattu na tsagin Turaki, Sanata Adolphus Wabara, da wasu mambobi ne suka shigar da ƙarar suna neman a umarci INEC ta amince da kwamitin tare da wallafa sunayen shugabanninsa. Sai dai tsagin Abdulrahman Mohammed mai samun goyon bayan Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ƙalubalanci ƙarar yana mai cewa shi ne halastaccen shugabancin PDP.
