Jam’iyyar ADC ta bayyana shakku kan lafiyar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da cancantarsa ta ci gaba da jagorantar ƙasa, tare da yin kira ga Majalisar Tarayya da ta gudanar da bincike kan lamarin. Jam’iyyar ta danganta hakan da ce-ce-ku-cen da suka dabaibaye naɗe-naɗen mukamai a gwamnatin tarayya.
A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na jam’iyyar, Mallam Bolaji Abdullahi, ya fitar, ADC ta yi zargin cewa shugaban ya rasa iko kan gwamnatinsa. Ta ce rikicin shugabanci a Hukumar Raya Yankunan Kan Iyaka (BCDA), da batun Majalisar PFIPC da sauya wasu manufofin gwamnati, sun haifar da tambayoyi kan wanda ke amfani da ikon shugaban ƙasa wajen naɗa da sauke jami’ai.
Jam’iyyar ta ce ya kamata Majalisar Tarayya ta yi amfani da tanadin kundin tsarin mulki domin tantance ko shugaban na da cikakkiyar lafiya da ikon gudanar da aikinsa. Ta kuma ce idan shugaban ba zai iya tabbatar da cikakken iko kan gwamnatinsa ba, ya kamata ya yi murabus.
