Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya ta fara wani shiri na musamman na kwato makaman da ake riƙe da su ba bisa ka’ida ba, a wani ɓangare na matakan ƙarfafa tsaro gabanin babban zaɓen ƙasar da za a gudanar a shekarar 2027.

Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Olatunji Disu, ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Abuja, inda ya ce shirin na da nufin rage yawaitar makamai ba bisa ƙa’ida ba a hannun jama’a da kuma inganta zaman lafiya kafin gudanar da zaɓe.

IGP Disu ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin rundunar na tabbatar da tsaro da samar da yanayi mai cike da kwanciyar hankali yayin da ƙasar ke tunkarar babban zaɓen 2027.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version