Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta sake dakatar da jam’iyyar PDP daga gudanar da babban taronta na kasa da aka shirya yi a garin Ibadan, Jihar Oyo, a ranar 15 zuwa 16 ga watan Nuwamba.
Wannan na zuwa ne bayan kotu ta yi irin wannan umarni a baya, lamarin da ya hana jam’iyyar ci gaba da shirin taron da ake sa ran za a zabi sababbin shugabanni na jam’iyyar.
Haka zalika, kotun ta umarci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da kada ta sa ido ko ta amince da sakamakon duk wani taro da PDP za ta yi a wannan lokacin.
Sai dai a baya, wata kotu a jihar Oyo ta bayar da umarni akasin haka, inda ta ce jam’iyyar ta ci gaba da shirye-shiryen taron, abin da ya haifar da rashin tabbas a cikin jam’iyyar.
Mai shari’a Peter Lifu ne ya yanke wannan sabon hukunci a ranar Talata, bayan tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya shigar da ƙara yana neman a dakatar da jam’iyyar daga yin zaben sababbin shugabanni. Lamido ya zargi jam’iyyar da hana shi damar shiga takara.
Rahoton ya fito ne daga Channels Television.
