Babbar Kotun Najeriya ta bayyana rashin jin daɗinta kan rashin aiwatar da hukuncin da ta yanke a Yuli 2024, wanda ya umurci gwamnatin tarayya da ta biya kason kudi na kananan hukumomi kai tsaye daga Asusun Tarayya. Kotun ta ce babu wani hujja mai karfi da ke nuna cewa Lauyan Tarayya (AGF) ya kammala ko fara shirye-shiryen da suka dace don aiwatar da wannan hukunci.
A cikin hukuncin da aka yanke, Mai Shari’a Mohammed Idris ya bayyana cewa kason kudi na kananan hukumomi mallakar su ne kai tsaye, kuma gwamnati ta tarayya ko jihohi ba su da hurumin shiga harkokin su. Ya ce Ƙananan hukumomi su ne ke da ikon gudanar da asusun su, ciki har da karɓa da sarrafa kuɗin da aka ware musu. Hakazalika, ya umarci Gwamnatin Tarayya da ta fara aiwatar da hukuncin nan take, ta kuma saki duk wani kudi da ake bi.
A bangare guda, Mai Shari’a Emmanuel Agim, wanda ya yi gardama, ya goyi bayan ra’ayin Osun State AG, inda ya ce jiha na da hurumin gabatar da kara kan batun, saboda akwai takaddama tsakanin Osun da Gwamnatin tarayya game da rike kason kananan hukumomi.
A halin yanzu, Osun ALGON ta yi marhabin da hukuncin, tana mai cewa wannan nasara ce ga dimokiradiyya, kyakkyawan shugabanci, da kuma al’umma. Har ila yau, Majalisar Dokokin Osun ta kafa dokar “Osun State Local Government Account Administration Bill 2025” don tsara yadda za a bude da sarrafa asusun kananan hukumomi a bankuna, inda aka tanadi cewa masu mukamai na siyasa ba za su iya zama masu sanya hannu ba, sannan duk wanda ya saba zai fuskanci hukunci har zuwa shekaru biyar ko tara naira miliyan 50, ko duka biyun.
