Kotun Tarayya da ke Warri, Jihar Delta, ta ba da umarni ga Rundunar ‘Yan Sanda ta Najeriya da Sufeton ‘Yan Sanda na ƙasa da su ci gaba da bin tsarin da ake kai tun kafin a fara aiwatar da dokar tilasta neman lasisin gilashin mota mai duhu (tinted), har sai an kammala shari’a.

Rundunar ‘Yan Sanda ta farfaɗo da tsarin ne a watan Yuni 2025 ta hanyar tsarin dijital na POSSAP, bisa hujjar cewa masu laifi na amfani da motoci masu duhun gilashi wajen kauce wa bincike. An ba da wa’adin kwanaki 30, daga baya aka tsawaita zuwa watan Agusta sannan zuwa Oktoba domin ba direbobi damar yin rajista.

Sai dai lauya John Aikpokpo-Martins ya maka ‘yan sanda kotu, yana kalubalantar sahihancin tilasta tsarin bisa dokar 1991 da ke buƙatar “dalili mai kyau” kafin a bayar da lasisi. Lauyan da ƙungiyoyin farar hula da NBA suna zargin tsarin da keta ‘yancin dan adam, rashin gaskiya wajen karɓar kuɗaɗe da kuma yiwuwar cin zarafi daga jami’an tsaro.

‘Yan sanda sun ce tsarin yana da inganci kuma na tsaro ne, amma umarnin kotun ya nuna yadda ƙalubale daga jama’a da masana shari’a ke ƙaruwa. A halin yanzu, batun yana cikin ruɗani — direbobi ba su da tabbas ko za a ci gaba da aiwatar da tsarin ko a’a, har sai an yanke hukunci na ƙarshe.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version