Hukumar Kwastam ta Najeriya, reshen Seme, ta sanar da cafke haramtattun kaya da darajarsu ta kai Naira biliyan 1.99 tsakanin ranar 1 ga Satumba zuwa 9 ga Oktoba, 2025. Kayan sun haɗa da miyagun ƙwayoyi da kuma buhunan fulawa daga Masar waɗanda su ka lalace.

Shugaban hukumar a Seme, Wale Adenuga, ya bayyana cewa buhunan fulawa 10,000 da aka kama an ɗora su ne a cikin manyan motoci guda biyar. Ya ce idan aka bari fulawar ta shiga kasuwa, tana iya jawo matsalolin lafiya kamar guba da cututtuka masu tsanani.

Hukumar ta kuma kama jakunkunan wiwi 1,104 da fakiti 120 na tramadol, tare da mika mutane biyu ga hukumar NDLEA. Haka kuma an kama buhunan shinkafa na waje 2,043, tsofaffin kaya 150, syrup ɗin codeine 169. Adenuga ya bayyana wannan a matsayin “satar tattalin arziki” wadda ke rage wa ƙasa kuɗaɗen shiga tare da kawo barazana ga lafiyar jama’a.

Baya ga hakan, hukumar ta taimaka wajen fitar da kayayyaki (non-oil exports) da suka kai ton 53,989.46 zuwa kasashen waje, da kimanin darajar N7.9bn, a ƙarƙashin tsarin ETLS na ECOWAS. Haka kuma ta tara harajin N1.5bn a watan Satumba kawai — karin kashi 182 cikin 100 daga watan da ya gabata. Adenuga ya tabbatar da cewa za su ci gaba da haɗa fasaha da bayanan sirri domin tabbatar da tsaro da kuma inganta kasuwanci a iyakar.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version