Shugaba Tinubu Ya Naɗa Amupitan a Matsayin Sabon Shugaban INEC
Majalisar Koli ta kasa ta amince da nadin Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN) a matsayin sabon shugaban INEC, bayan kammala wa’adin Farfesa Mahmood Yakubu na shekaru 10.
Shugaba Bola Tinubu ya gabatar da sunan Amupitan ga majalisar yayin taron da aka gudanar a fadar shugaban kasa, Abuja. Amupitan, wanda dan jihar Kogi ne kuma lauya mai shekara 58, shi ne mutum na farko daga yankin Arewa ta Tsakiya da aka naɗa wannan mukami.
