Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Hana Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC) ta bayyana cewa ta fara gudanar da cikakken bincike kan zargin karkatar da wasu kuɗaɗe sama da naira biliyan huɗu da ake tuhumar tsohuwar gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje da hannu a ciki. Shugaban hukumar, Saidu Yahaya, ya ce binciken ya samo asali ne daga wani ƙorafi da aka shigar kan yadda aka fitar da kuɗin gwamnati aka saka su a cikin asusun Dala Inland Dry Port.
A cewar Yahaya, an ɗauki kuɗaɗen ne a zamanin mulkin tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, kuma yanzu hukumar na gudanar da cikakken bincike domin gano yadda aka yi amfani da su da kuma mutanen da ke da hannu a lamarin.
Sai dai tsohon kwamishinan yaɗa labarai na jihar kuma tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Ganduje, Muhammad Garba, ya bayyana cewa lamarin yana gaban kotu, don haka ba zai yi wani tsokaci kai tsaye ba. Ya ce wannan bincike ba sabon abu ba ne domin ana yawan gudanar da irin sa a wurare daban-daban.
