Rundunar ’yan sandan Jihar Gombe ta kama wani matashi mai shekara 19, Shuaibu Adamu, bisa zargin kashe wani abokin aikinsa a harabar Gidan Gwamnati. Lamarin ya faru ne a ranar 26 ga Disamba, inda mamacin, Mallam Umar da ake kira Baba Usama, ya mutu bayan wani hari da aka kai masa.
Mai magana da yawun ’yan sandan jihar, Buhari Abdullahi, ya ce sun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 3:50 na rana, inda aka samu mamacin a kwance babu rai. An garzaya da shi Asibitin Kwararru na Gombe, amma likita ya tabbatar da mutuwarsa, lamarin da ya sa Kwamishinan ’yan sanda ya umarci a fara bincike mai zurfi.
Binciken farko da kuma duba faifan CCTV ya nuna cewa wani ma’aikaci ne ya kai masa hari kafin mutuwarsa. An gano Shuaibu Adamu a matsayin babban wanda ake zargi, inda aka kama shi a Bagadaza Quarters a daren ranar, kuma ya amsa laifin. ’Yan sanda sun ce za a gurfanar da shi gaban kotu bayan kammala bincike.
