Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da naɗin Janar Christopher Musa a matsayin sabon Ministan Tsaro, bayan wani zaman da ya cika da hayaniya da ƙorafe-ƙorafe daga ‘yan majalisa. Wasu senatocin sun zargi Janar ɗin da ƙoƙarin wucewa ba tare da amsa tambayoyi masu muhimmanci ba.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya tsoma baki domin kwantar da tarzoma, inda ya ce dole ne wanda ake tantancewa ya amsa tambayoyin da suka shafi tsaro yadda ya kamata. Ya kuma jaddada cewa ba lokacin siyasar “rusuna ka wuce” ba ne, musamman ga wanda ya taɓa riƙe babban mukamin tsaro a ƙasar.
A cikin jawabinsa, Janar Musa ya bayyana tsare-tsaren da zai bi domin farfaɗo da martabar rundunar soji da kuma magance matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar. Janar ɗin ya yi alƙawarin yin aiki kafada-da-kafada da hukumomi domin tabbatar da zaman lafiya da kariyar rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa.
Ana sa ran sabon ministan zai fara aiki nan da nan, bayan saukar Mohammed Badaru daga muƙamin a ranar Litinin. ‘Yan Najeriya da dama na sa ran cewa wannan sabon sauyi zai kawo ɗaura damara wajen tunkarar ƙalubalen tsaro da ake fama da su a sassa daban-daban na ƙasar.


