Majalisar Dokokin Najeriya ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta fito fili ta bayyana sunayen masu daukar nauyin ta’addanci da garkuwa da mutane a ƙasar. Majalisar Dattawa ta kuma amince da dokar da ta mayar da satar mutane cikin laifin ta’addanci tare da hukuncin kisa ga masu aikatawa da masu ba su bayanai.

A yayin tattaunawar, sanatoci da yawa sun goyi bayan hukunci mai tsauri don dakile yawaitar sace mutane a jihohi, musamman bayan hare-haren da suka addabi makarantu da kauyuka. Majalisar Wakilai ma ta bukaci a kafa kotu ta musamman don shari’ar ta’addanci.

Tsohon Babban Hafsan Tsaro, Gen. Christopher Musa, ya sha tambayoyi kan gazawar tsaro da harin da ya kai ga sace dalibai 26 a Kebbi. Musa ya yi alkawarin bincike, karin hadin gwiwa, da karfafa tsaron makarantu, yana mai cewa Najeriya na fuskantar barazana daga kungiyoyi masu samun kudade ta hanyar hakar ma’adinai da sauran hanyoyi marasa doka.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version