Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da sabon kudirin doka da ke tanadar da hukuncin ɗaurin rai da rai ga duk wanda aka same shi da laifin lalata da yara ƙanana. Wannan mataki na zuwa ne sakamakon ƙaruwa da ake samu a aikata laifin cin zarafin yara a ƙasar, wanda ke barazana ga lafiyar su ta jiki da ta hankali.

Sanata Adams Oshiomhole daga Edo Arewa ne ya gabatar da kudirin, inda ya ce laifin lalata da yara ya fi muni saboda yara ba su da ikon yarda da irin wannan abu. A da farko, ya nemi hukuncin shekaru 20 a kurkuku, amma wasu sanatoci sun nemi a tsaurara hukuncin. Sanata Muhammad Aliero daga Kebbi ta Tsakiya ya gabatar da gyara, yana mai cewa hukuncin ya zama ɗaurin rai da rai ba tare da bambanci ba.

Shawararsa ta samu goyon bayan sanatoci da dama, ciki har da Sanata Solomon Adeola, sannan shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio, ya tabbatar da amincewa da kudirin ta hanyar kada kuri’ar murya. Idan shugaban ƙasa ya rattaba hannu, wannan doka za ta maye gurbin tsoffin tanade-tanaden da ke sauƙaƙa wa masu aikata laifin, tare da zama gargaɗi ga masu lalata da yara a Najeriya.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version