Majalisar dokokin jihar Kano ta janye tuhume-tuhumen da take yi wa tsohon Mataimakin Gwamna, Aminu Abdussalam Gwarzo, bayan da ya sauka daga mukaminsa.
Shugaban majalisar, Jibrin Isma’il Falgore, ne ya jagoranci zaman da aka yanke wannan hukunci, inda aka amince da dakatar da duk wani matakin tuhuma da ake yi a kansa.
Shugaban masu rinjaye a majalisar, Lawan Husaini Cediyar Yan’gurasa, ya bayyana cewa majalisar ba ta da ikon ci gaba da tuhumar Gwarzo, ganin cewa ya daina rike mukamin Mataimakin Gwamna.


