Majalisar Wakilai ta Najeriya ta bayyana cewa ba ta amince da iƙirarin da Amurka ta yi ba na cewa ana kashe Kiristoci a ƙasar saboda addini, tana mai cewa wannan labari ba gaskiya ba ne kuma yana iya haifar da ruɗani. Majalisar ta jaddada cewa matsalolin tsaro da ake fuskanta a Najeriya ba su da alaƙa kai tsaye da addini, sai dai suna da tushe da zamantakewa, siyasa da tattalin arziki.

Wannan martani ya fito ne yayin zaman majalisar na ranar Laraba 08 ga Oktoba, bayan gabatar da ƙudiri daga mataimakin kakakin majalisar, Benjamin Okezie Kalu, tare da wasu ‘yan majalisa. Sun nuna damuwa kan wani ƙudirin doka da Majalisar Dattawan Amurka ke shirin tattaunawa, wanda ke neman saka Najeriya cikin jerin ƙasashen da ke take hakkin ‘yancin addini.

Majalisar ta bukaci a samu haɗin kai tsakanin hukumomin diflomasiyya da na cikin gida domin amsa irin waɗannan zarge-zarge ta hanya mai ma’ana da hujjoji. Ta ce wajibi ne Najeriya ta kare sunanta a idon ƙasashen waje ta hanyar nuna gaskiyar halin da ake ciki.

A kwanakin baya ne Sanata Ted Cruz daga Amurka ya gabatar da ƙudiri domin kare Kiristoci a Najeriya daga abin da ya kira cin zarafi da kisa saboda addini, abin da ya tayar da hankalin hukumomin Najeriya da suka ce wannan ra’ayi bai nuna cikakken yanayin rikice-rikicen ƙasar ba.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version