Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar ADC za su koma APC a mako mai zuwa, yayin da jam’iyyar ke ci gaba da karɓar sabbin mambobi daga sauran jam’iyyun adawa kafin babban zaɓen 2027.
Yilwatda ya bayyana haka ne a yayin ganawarsa da mambobin jam’iyyar APC a Jos, Jihar Filato, inda ya ce waɗanda za su sauya sheƙa daga ADC sun riga sun kammala shirye-shiryensu kuma za a tarbe su a hukumance. Ya ce wasu daga cikin su sun bar PDP zuwa ADC a baya, amma yanzu sun yanke shawarar komawa APC.
Ya ƙara da cewa, akwai wasu fitattun ’yan siyasa da suka haɗa da gwamnoni, sanatoci da ’yan majalisa da dama da ke shirin shiga jam’iyyar a makonni masu zuwa. Ya ce za a bayyana sunan wani babban ɗan siyasa da ya kammala shirin sauya sheƙarsa cikin makonni biyu masu zuwa.
Shugaban jam’iyyar ya bayyana APC a matsayin “amaryar siyasa ta yanzu” wadda ke maraba da kowa, inda ya jaddada cewa duk wanda ya shiga jam’iyyar yana da cikakken haƙƙi da damar da sauran mambobi ke da ita, komai matsayin sa a baya.
