Gwamnatin Jihar Kogi ta sanar da rasuwar wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar APC guda uku a jihar. Mutanen da suka rasu sun hada da Hon. Onojah James Ignatius, Hon. Jatto Onimisi Suleiman da kuma Alhaji Alih Atabo, kamar yadda kwamishinan yada labarai da sadarwa na jihar, Kingsley Fanwo, ya bayyana a Lokoja.
A cewar sanarwar, marigayi Onojah James Ignatius ya kasance mashawarci na musamman ga gwamnan jihar kuma tsohon shugaban karamar hukumar Igalamela, yayin da Jatto Onimisi Suleiman ke rike da mukamin mataimakin mashawarci na musamman. Alhaji Alih Atabo kuwa shi ne shugaban APC na mazabar Anyigba a karamar hukumar Dekina.
Gwamnatin jihar ta bayyana cewa mamatan sun yi wa jihar Kogi da jam’iyyar APC hidima da kwarewa da rikon amana. Gwamna Ahmed Usman Ododo ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalai, ‘yan uwa da daukacin jam’iyyar APC, yana mai cewa gudunmawarsu ga ci gaban jihar ba za a manta da ita ba.
