Kamfanin Dangote ya bayyana shirinsa na sake tura injiniyoyin da aka sallama daga matatar man sa zuwa sauran sassan kasuwancinsa, musamman masana’antun sukari da siminti, bayan rikicin da ya barke da ƙungiyar ma’aikata ta PENGASSAN. Rahotanni sun bayyana cewa ma’aikatan sun kasance daga cikin injiniyoyin farko da suka taimaka wajen gina da kaddamar da babbar matatar man Dangote da ke Legas — wacce ita ce mafi girma a Afirka — kafin a sallame su bisa zargin yin leƙen asiri da aikata ayyukan da ke barazana ga kamfanin.
Rikicin ya fara ne bayan PENGASSAN ta zargi kamfanin da sallamar ma’aikata 800 saboda shiga ƙungiyar kwadago, abin da ya haifar da yajin aiki a fannin mai da iskar gas wanda ya janyo asarar tattalin arziki da raguwa a samar da wuta. Kamfanin Dangote ya musanta wannan zargi, yana mai cewa kawai ’yan kadan ne aka kora saboda laifin satar bayanan sirri. Gwamnatin tarayya ta shiga tsakani, inda aka cimma matsaya cewa a sake tura waɗanda abin ya shafa zuwa wasu rassan kasuwancin kamfanin.
Wasu daga cikin injiniyoyin da aka sallama an ce an horar da su ne a ƙasashen waje domin aikin matatar, kuma kamfanin ya yi asarar manyan ƙwararru da ya ɗauki lokaci da kuɗi wajen horarwa. An bayyana cewa wasu za a tura su zuwa rassan kamfanin a ƙasashen waje, yayin da wasu kuma za su koma aiki a masana’antun cikin gida. A lokaci guda, kamfanin ya shirya ɗaukar sabbin injiniyoyi domin cike gibin da aka bari.
Matatar Dangote ta fuskanci suka daga ƙungiyoyin ma’aikata da ’yan kasuwa a ’yan makonnin da suka gabata, musamman kan batutuwan albashi, tsarin kasuwanci, da ’yancin ma’aikata. Duk da shawarwarin gwamnati da aka cimma don kawo sulhu, masu ruwa da tsaki na jiran yadda kamfanin zai aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma tsakaninsa da ƙungiyoyin ma’aikata.
