Matatar Dangote ta ƙara farashin man fetur daga naira 774 zuwa naira 874 kan kowacce lita, matakin da ya jawo fargaba kan yiwuwar tashin farashi a faɗin Najeriya. Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa wani jami’in matatar ya ce an ɗauki matakin ne sakamakon hauhawar farashin mai a duniya da rikicin Gabas ta Tsakiya ya haddasa.
Binciken shafin petroleumprice.ng ya nuna an fara amfani da sabon farashin, lamarin da zai iya shafar dillalai da masu amfani da fetur baki ɗaya. Ƙarin farashin ya biyo bayan dakatar da lodin fetur da matatar ta yi daga 12 na dare, 2 ga Maris, 2026, bayan farashin ganga ya haura dala 80 cikin dare.
Masu sayar da fetur sun nuna fargabar yiwuwar ƙarancin mai a wasu yankuna, musamman a lokutan buƙata mai yawa. Masana tattalin arziki kuma sun yi gargaɗin cewa tashin farashin na iya janyo hauhawar wasu kayayyaki da tsananta matsin rayuwa ga al’umma da ‘yan kasuwa a Najeriya.


