Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa rufe Matatar Mai ta Fatakwal na tsawon watanni biyar daga watan Mayu zuwa Oktoba 2025 ya janyo wa Najeriya asarar fiye da Naira Biliyan N366.2, wanda ya yi daidai da dala miliyan 249.7. Wannan matata, wadda aka ce tana da ƙarfin tace gangar mai 60,000 a rana, ta fara aiki a karshen 2024 bayan an kashe dala biliyan 1.5 wajen gyaranta, amma aka sake rufeta don “gyaran dindindin” bayan watanni shida kacal.

Sai dai wasu ma’aikatan matatar sun bayyana cewa tun bayan bude ta a 2024 har zuwa lokacin da aka rufe ta, ba a taɓa tace mai a cikinta ba, inda suka zargi shugabannin kamfanin NNPCL da amfani da kayayyakin da aka kawo daga wasu wurare a matsayin kayan da suka tace. Sun ce an hana ma’aikata yin magana da ’yan jarida domin kada gaskiya ta bayyana. Shugaban kamfanin NNPCL, Bayo Ojulari, ya tabbatar cewa kamfanin yana asara tsakanin N300m zuwa N500m a wata, yana mai cewa matsalar matatar ta samo asali ne daga tsarin da aka gurbata shekaru da dama.

Kungiyar ma’aikatan masana’antu (NAPO) da kuma ’yan kasuwar man fetur (IPMAN) sun zargi rashin gaskiya, siyasa, da tasirin masu kamfanonin mai na kashin kansu da hana matatar yin aiki yadda ya kamata. Sun nemi gwamnati ta mika gudanarwar Matatar ga kwararrun kamfanonin, tare da gargadin cewa rashin aikin Matatar yana janyo asarar ayyuka da kudaden shiga ga kasa da al’umma.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version