A ranar Litinin, 1 ga Disamba 2025, Ministan Tsaron Najeriya, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya ajiye aikinsa nan take bisa dalilan lafiya. Wasikar murabus ɗin, wacce aka turawa Shugaba Bola Tinubu, ta tabbatar da cewa ya yanke shawarar hakura da mukaminsa domin kula da lafiyarsa.
Shugaba Tinubu ya amince da murabus ɗin tare da gode masa bisa hidimar da ya yi wa ƙasa tun lokacin da aka naɗa shi a ranar 21 ga Agusta 2023. Rahotanni sun nuna cewa shugaban ƙasar zai sanar da majalisar dattawa sabon ministan tsaro cikin mako ɗaya mai zuwa domin ci gaba da aiki ba tare da tsayawa ba.
Badaru, tsohon gwamnan jihar Jigawa sau biyu, ya bar kujerar ne a daidai lokacin da Shugaba Tinubu ya bayyana dokar ta-baci kan harkokin tsaro a fadin ƙasar. Ana sa ran gwamnati za ta fayyace matakan da wannan dokar ta ƙunsa nan gaba kaɗan.
Murabus ɗin Badaru ya jawo ce-ce-ku-ce a fagen siyasa ganin rawar da yake takawa a tsarin tsaro. Yanzu idanu sun koma kan matakin da shugaban ƙasa zai ɗauka wajen cike gurbin da aka bari, da kuma yadda hakan zai shafi tsarin tsaro a sabon yanayin gaggawa da gwamnati ta ayyana.
