Rundunar ‘Yan Sanda ta Ƙasa ta dakatar da aiwatar da dokar kama direbobin da basu mallaki lasisin gilashin mota mai duhu (tinted permit), bayan karbar wani umarni daga kotu da ya hana ci gaba da wannan aikin.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta babban birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, ta bayyana hakan a hirar da ta yi da tashar AIT ranar Laraba 08 ga Oktoba. Ta tabbatar da cewa rundunar ta karɓi umarnin kotu, kuma hakan ya sa aka dakatar da duk wani matakin tilasta wa direbobi takardar tinted har sai an kammala shari’ar da ke gaban kotu.

“An dakatar da aiwatar da wannan doka ne saboda umarnin kotu. Rundunar ba za ta ci gaba da aiki a kan lamarin ba sai an samu hukuncin karshe,” in ji Adeh.

Ta kara da cewa manufar kafa dokar tinted ba ta kudi ba bace, illa dai don tsaro — saboda wasu miyagu na amfani da motoci masu gilashi mai duhu wajen aikata laifuka, lamarin da ke wahalar da jami’an tsaro gane su.

Haka kuma, ta bayyana cewa kudaden da ake biya don samun izinin tinted ana tura su ne kai tsaye zuwa Asusun Gwamnatin Tarayya (TSA), ba hannun ‘yan sanda ba.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version