Jam’iyyar PDP ta caccaki gwamnoninta da suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC, tana zarginsu da son kai da kwaɗayi, tare da jaddada cewa jama’a ne za su yanke musu hukunci a zaben 2027. PDP ta ce ba gwamnonin ne ke gina jam’iyya ba, sai talakawa, don haka sauya sheƙar ba zai tarwatsa ta ba. Tun bayan zaɓen 2023, gwamnonin jihohin Delta, Akwa Ibom, Enugu da Bayelsa sun fice daga jam’iyyar, haka ma tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da abokin takararsa Ifeanyi Okowa duk sun bayyana ficewa daga jam’iyyar. Kakakin jam’iyyar na ƙasa, Ibrahim Abdullahi, ya bayyana sauya shekar a matsayin alamar son kai da rashin kishin jam’iyya, yana mai cewa PDP tana ci gaba da shiri domin babban taronta a Ibadan wanda zai “sake fasalin jam’iyyar” kafin 2027.

Shugabannin PDP sun kuma yi zargin cewa gwamnoni na ficewa ne saboda matsin lamba daga jam’iyyar APC. Shugaban rikon kwarya na yankin Kudu maso Kudu, Elder Emmanuel Ogidi, ya ce ana tilasta wa gwamnoni da mambobin jam’iyya su fice don raunana PDP, tare da gargadin cewa APC na ƙoƙarin mayar da Najeriya jam’iyya ɗaya. Sai dai APC da fadar shugaban ƙasa sun musanta wannan zargi, suna cewa PDP ce ta haifar da matsalolinta.

A gefe guda, Farfesa Udenta O. Udenta ya kira gwamnonin da suka sauya sheƙa “marasa ƙarfin hali”, yana mai cewa sun kasa tsayawa tsayin daka wajen kare jam’iyyarsu da ƙa’idar tsarin tarayya. Ya ce shugabanni na gaskiya suna shawo kan rikice-rikicen cikin gida ba tare da gudu ba. Udenta ya yi nuni da yadda Tinubu ya fuskanci gwamnatin PDP a matsayinsa na gwamnan Legas tsakanin 1999 da 2007, yana mai cewa sabbin gwamnonin ba su da irin wannan jajircewa. Ya kuma yi kira ga ‘yan ƙasa su kare tsarin jam’iyyu masu yawa don guje wa rugujewar dimokuraɗiyya.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version