Masana harkar noma sun bayyana cewa mutane biyu cikin kowace goma sha ɗaya a Najeriya na fama da yunwa a kullum, yayin da ɗaya cikin biyar na nahiyar Afirka ke fama da ƙarancin abinci.
Wannan bayani ya fito ne daga Onijighogia Emmanuel, wakilin shirin Comprehensive Africa Agriculture Development Programme (CAADP) na kasa, yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Abuja kan aiwatar da Yarjejeniyar Kampala ta Tarayyar Afirka.
Yarjejeniyar, wadda shugabannin ƙasashen Afirka suka amince da ita a Janairu 2025, na da nufin canza tsarin noma da abinci a nahiyar cikin shekaru goma masu zuwa (2026–2035).
Emmanuel ya bayyana cewa kaso 58% na Afirka ke fama da matsananciyar rashin abinci, inda mutane miliyan 924.8 ba su iya samun abinci mai gina jiki. A Najeriya kuma, kusan gida 6 cikin 10 ba sa iya cin abinci mai kyau. Ya kuma nuna cewa sama da mutane 50,000 a Najeriya na kamuwa da cututtuka saboda abinci mara tsabta a duk shekara.
Duk da cewa ƙasashen Afirka sun kuduri niyyar ware 10% na kasafin kuɗi ga noma, Najeriya na kashe kusan 3% kacal. Sai dai ya yaba da ƙoƙarin ma’aikatar noma wajen kafa kwamiti na musamman domin tsara sabon shirin shekaru goma.
A nasa jawabin, Azubike Nwokoye na ActionAid ya jaddada muhimmancin tabbatar da gaskiya da bin doka wajen aiwatar da yarjejeniyar Kampala. Ya bukaci a samar da bashi ga manoma, kayan zamani, a inganta ajiya da sarrafa amfanin gona, tare da shigar da mata da matasa sosai cikin harkokin noma.
Grace Oyediji, shugabar ƙungiyar ƙananan manoman mata, ta bukaci gwamnati ta ƙara saka hannun jari a fannin noma da sauƙaƙa samun bashi. Ta ce, “Manoma ba sa son yin yajin aiki, domin idan muka tsaya, babu wanda zai ci abinci.”
Rahotanni sun nuna cewa Najeriya na cikin mummunan halin talauci, inda mutane miliyan 133 ke fama da rashin abinci, ruwa, ilimi, da kula da lafiya — lamarin da ya tsananta bayan cire tallafin mai da daidaita naira a 2024.
